Shafin 1 na 1

Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (3)

An buga: Litini Feb 09, 2026 1:48 am
by MediaHausa
*Legacy Post Number 85 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (3)
Timeline: 2012-06-19 02:41:14


Fatawoyin Aikin Hajji Da Umra Da Ziyara (3)

A Rubuce Da Sheikh Abdulwahhab Abdullah

A makon jiya mun buga huduba a wannan shafi a maimakon Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da muka fara gabatarwa mako uku da suka gabata. Wannan gazawa ce irin tad an Adam. Da fatar za a gafarce mu .Yau ga ci gaba daga inda muka tsaya a makon shekaranjiya:

Tambaya ta 9: Me ya kamata maniyyaci ya fara yi kafin tafiya?

Amsa: Abubuwan da maniyyaci ya kamata ya fara yi su ne:

1. Kyautata niyyarsa da ikhlasi, watau, ya kudurta cewa zai je ya yi wannan ibada ce don neman yardar Allah, ba don riya ko neman duniya ko son a sani ba.

2. Ya tabbatar dukiyar da zai yi aikin Hajji da ita ta halal ce.

3. Lallai ne ya nemi sanin hukunce-hukuncen Hajji, domin ba a bauta wa Allah a cikin rashin sani.

4. Haka kuma lallai ne mutum ya nemi afuwa daga duk wanda ya san ya shiga hakkinsa, na mutunci ko na dukiya. Idan ana bin sa bashi, ya yi kokarin biya, ko ya nemi a yafe masa, ko kuma a yi masa lamuni har sai ya dawo.

5. Idan akwai abin da yake son yin wasiyya da shi, ya hanzarta yin hakan kafin ya tafi.

6. Sannan kuma lallai ne ya nemi abokan tafiya nagari, wadanda zai koyi kyawawan dabi’u da ilimi daga gare su, domin kuwa zama da madaukin kanwa, shi ke kawo farin kai.

7. Kuma ya sani cewa duk mutanen da zai hadu da su a wurin aikin Hajji ’yan uwansa ne Musulmi, kada ya nuna musu bambancin kabila ko launi ko yare. Domin haka, sai ya yi mu’amala mai kyau da su, tare da tausasawa da hakuri da rahama da afuwa gare su.

Tambaya ta 10: Mutumin da Allah Ya ba shi ikon da zai je aikin Hajji, amma iyayensa ba su samu ikon zuwa ba, shin zai fara gabatar da su ne, ko kuwa shi zai fara zuwa?

Amsa: Shi zai fara sauke nauyin da ke kansa, saboda shi ne Allah Ya ba ikon, kuma Allah Ya wajabta aikin Hajji ne ga wanda yake da iko. Ya kamata mu sani cewa a cikin rukunan Musulunci guda biyar, babu wanda aka ce a fara gabatar da iyaye. Ubangiji Ya ce: “Allah Ya wajabta aikin Hajji a kan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa a gare shi...” Al-Imran: aya ta 97.

Saboda haka, idan mutun ya sauke farillarsa, babu wanda ya fi cancanta ya biya wa kamar iyayensa. Amma idan Ubangiji Ya ba shi halin tafiya tare da iyayensa, to, sai su tafi gaba daya. Yin hakan, shi ya fi alheri.

Tambaya ta 11: Mutumin da ya dauki adashi, zai iya zuwa aikin Hajji da shi kafin ya biya sauran zubin da ake binsa?

Amsa: Na’am, zai iya zuwa aikin Hajji da shi, idan abokan adashin sun lamunce masa, kamar dai hukuncin wanda ake binsa bashi. Dalili kuwa shi ne, fadin Ubangiji cewa: “Ga wanda yake da ikon zuwa...” Al-Imran: aya ta 97.

Shi kuwa ba zai samu iko ba, har sai ma su bin sa adashi ko bashi sun lamunce masa.

Tambaya ta 12: Shin mace mai takaba za ta iya zuwa aikin Hajji?

Amsa: A’a, bai halatta ba ga mace mai takaba ta tafi aikin Hajji, domin shari’a ta umarce ta da lazimtar dakinta. Saboda haka, ba za ta fita ba, sai da larurar da shari’a ta yarda da ita (kamar zuwa asibiti don neman magani, ko yin sana’a idan babu wanda ke daukar nauyinta, ko ta je ta debo amfanin gonarta, idan babu wanda zai debo mata). Dalili kuwa shi ne abin da ya tabbata daga Imam Mujahid cewa: “Hakika Sayyadina Umar Ibnul

Khaddab da Sayyadina Usman Ibnu Affan (RA) suna mayar da mata masu takaba wadanda suka nufi aikin Hajji ko Umara gidajensu, har sai sun gama takaba a gidajensu. Duba Musannaf Ibnu Abu Shaibah: Juzu’i na uku, Shafi na 326, hadisi na 14647; da Musannaf Abdurrazak: Juzu’i na 7, Shafi na 33, Hadisi na 12070; da kuma al-Istizkar na Ibnu Abdul-Barr, Juzu’i na 18, Shafi na 182, Hadisi na 1214. Amma wannan lafazin na Ibnu Abu Shaibah ne.

Amma akwai magana ta biyu da ake dangana ta ga Nana A’isha cewa mai takaba ko idda za ta iya tafiya aikin Hajji ko Umara. Har ma an samu cewa Nana A’isha (RA) ta fita zuwa Umara tare da kanwarta Ummu Kulsum (RA), wadda take cikin takaba. 22. Duba al-Istizkar na Ibnu Abdul-Barr, Juzu’i na 18, Shafi na 184, Mas’ala ta 27425 da na 27426.

Imam Ibnu Abdul-Barri ya hakaito cewa kasim Ibnu Muhammad ya ce: “Mafi yawan sahabbai da wadansu daga cikin tabi’ai na zamaninta, sun yi wa Nana A’isha (RA) inkari a kan wannan fatawar. Duba al-Istizkār na Ibnu Abdul-Barr, Juzu’i na 18, Shafi na 185, Mas’ala ta 27428.

Kuma shi ne zance mafi rinjaye a wajenmu. Amma malamai sun ce idan mace ta fita zuwa aikin Hajji ko Umara, sai ta samu labarin mutuwar mijinta, alhali tana kusa da gari, to, sai ta dawo ta yi iddarta. Idan kuwa ta yi nisa, sai ta ci gaba da aikin Hajjinta ko umararta, kuma wannan shi ne kaulin Imamus Shafi’i da Imam Abu Hanifah (Allah Ya yi musu rahama). Duba littafin al-Mugni na Ibnu kudamah al-Makdisi, tahkikin Dokta Abdullah Ibnu Abdul Muhsin At-Turki, Juz’i na 24, Shafi na 164, Bugun Daru Alamul Kutub.

Amma idan idda ce ta saki, to, ba za a hana ta zuwa aikin Hajjin ba, matukar dai da izinin mijinta idan saki daya ne ko biyu ko kuma izinin waliyyinta idan saki uku ne.

Tambaya ta 13: Yaushe ne maniyyaci zai dauki niyyar aikin Hajji, kuma a ina zai dauka?

Amsa: Maniyyaci zai dauki niyya ne a mikati yayin da ya daura ihraminsa, kuma zai kudurta niyyarsa ce tare da talbiyya. Hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibnu Umar (RA) ya ce: “Hakika Manzon Allah ya kasance idan ya daidaita a kan abin hawansa, alhali tana tsaye a wajen Masallacin Zul Hulaifa, sai ya daga murya da talbiyya, ya ce: Labbaikal Lahumma Labbaik, Labbaika La Sharika Laka Labbaik, Innal Hamda, Wan Ni’amata Laka Wal Mulka, La Sharika Laka.” Sahih Muslim: Kitabul Hajji, Babut Talbiyyati, wa Sifatiha, wa Waktiha, Hadisi na 1184.

A wannan lokacin ne zai furta niyyar nau’in irin Hajjin da zai yi, ko dai na Tamattu’i ko na kirani ko kuma na Ifradi. Misali idan Tamattu’i yake son ya yi harama da shi, to zai fara ne da harama da yin Umarah ya ce: “Labbaikal Lahumma Labbaika Bil Umrah!”

(Amma mu tuna fa mai Tamattu’i sai a Makkah ranar da za a fita zuwa Mina zai yi haramar Hajji), sai ya ce: “Labbaikal Lahumma Labbaika Bil Hajji!”

Idan kuma kirani yake son ya yi harama da shi, wato ya hada Hajji da Umarah, to, sai ya ce: “Labbaikal Lahumma Labbaika bil Hajji wal Umrah!”

Idan kuma Ifradi yake son ya yi, wato wanda zai yi harama da Hajji shi kadai, to, sai ya ce: “Labbaikal Lahumma Labbaika Bil Hajji!”

Za mu ci gaba insha Allahu.


**{Legacy activities, comments etc counter: 830; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}